A cewar rahoton sashen fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza, a yayin wannan ganawar, an tattauna batutuwa da dama da suka shafi bil'adama a matakin kasa da kasa, da kuma sabbin sauye-sauyen da ke faruwa a yankin. Ayatullah Sheikh Bashir Hussain Najafi, a cikin jawabinsa, ya jaddada nauyin da ya rataya a wuyan ayyukan diflomasiyya, inda ya bayyana cewa: "Ya kamata ofisoshin Tarayyar Turai a Iraki su gudanar da ayyukansu ta hanyar da za ta kasance hidima ta gaskiya ga al'umma da kuma maslahar jama'a."
Haka nan kuma, ya jaddada muhimmancin taka rawar gani na Tarayyar Turai wajen kyautata yanayin kasar Iraki a fannoni daban-daban da suka hada da tattalin arziki, ilimi, da al'amuran zamantakewa. Ya kara da cewa: "Hadin gwiwar kasa da kasa zai samar da sakamako mai kyau ne kawai idan aka gina shi a kan zurfafa fahimtar ainihin bukatu na al'umma da kuma girmama dabi'u da karfin da mutanen yankin suke da shi."
Ayatullah Bashir Najafi ya yi nuni da muhimmancin girmama asalin al'umma da gadon wayewarsu, inda ya bayyana cewa: "Mutanen Iraki magada ne na tsohuwar wayewa mai tushe, wacce tarihinta ya samo asali tun farkon bayyanar wayewar dan'adam; don haka, dole ne hukumomi da kungiyoyin kasa da kasa su rika la'akari da wannan gaskiya ta tarihi da al'ada a lokacin da suke hulda da Iraki."
A nasa bangaren, Clemens Semtner, jakadan Tarayyar Turai a Iraki, ya gabatar da rahoton ayyuka da nauyin da ya rataya a wuyan tawagar diflomasiyyar tasu a Iraki, inda ya ce: "Tarayyar Turai tana daukar zaman lafiya, ci gaba mai dorewa, da kuma inganta rayuwar al'ummar Iraki a matsayin daya daga cikin abubuwan da ta sa a gaba, kuma a wannan tafarkin, tana kallon hadin gwiwa da tattaunawa da cibiyoyin addini da na zamantakewa a matsayin babban al'amari."
Daga karshe, ya nuna godiyarsa ga Ayatullahil Uzma Sheikh Bashir Hussain Najafi saboda kyakkyawan tarbar da ya yi musu da kuma ware lokacinsa don wannan ganawar.
Your Comment